Duniya ta yi tur da sace 'yan matan Chibok

Shugaban Amurka Barack Obama Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sama da makonni uku kenan da kungiyar Boko Haram ta sace 'yan matan a makarantar sakandare ta Chibok

Ana samun karin martani na kasashen duniya game da sace 'yan mata sama da 200 'yan makarantar Chibok a jihar Borno a Nigeria.

Amurka da Birtaniya sun yi wa Nigeria tayin taimaka mata wajen tabbatar da sakin 'yan matan.

Yayin da manyan mutane kamar Hillary Clinton da Winnie Mandela su ma suka sa baki, domin ganin an saki daliban da kungiyar Boko Haram ta sace.

Shi ma shugaban kasar Ghana John Mahama, ya bai wa shugaban Najeriya Goodluck Jonathan tabbacin goyon bayan kungiyar ECOWAS, domin yaki da kungiyar Boko Haram.

Karin bayani