'Ayyukan 'yan Boko Haram abin kyama ne'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption William Hague ya ce za su taimakawa Nigeria

Sakataren harkokin wajen Birtaniya, William Hague ya bayyana ayyukan 'yan Boko Haram a Nigeria a matsayin abin "kyama da kuma Allah wadai".

Mr Hague ya ce Birtaniya za ta taimakawa hukumomin Nigeria don ganowa da kuma ceto dalibai 'yan mata da aka sace makonni uku da suka wuce a makarantarsu.

Ita ma Amurka ta bayyana takaicinta kan batun, inda ta ce Shugaba Obama na samun bayanai game da lamarin.

A waje daya kuma kungiyoyi da dama a fadin duniya sun nuna goyon baya ga iyayen 'yan matan da aka sace inda suke yin zanga-zangar lumana.

Gwamnatin Nigeria ta ce za ta yi iyaka kokarin don ganin cewar an kubutar da 'yan matan daga hannun 'yan Boko Haram.

Kungiyar Boko Haram ta ce ita ce ta sace 'yan mata kuma za ta sayar da su a matsayin bayi.

Karin bayani