Harkoki sun tsaya cik a majalisar dokokin Nijar

Hamma Amadou, Shugaban Majalisar dokokin Nijar Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Hamma Amadou, Shugaban Majalisar dokokin Nijar

A jamhuriyar Niger bangaren masu rinjaye na 'yan majalisar dokoki sun zargi shugaban majalisar dokokin kasar, Malam Hama Amadu da taka doka, lamarin da suka ce, ya tauye ayukkan majalisar.

Tuni dan bangaren masu rinjayen suka shigar da wata kara gaban.

kotun tsarin mulki yau din nan suna neman ta tabbatar da cewa Hama Amadu din ne ke hana ruwa gudu.

Sai dai a nasu bangare magoya bayan shugaban majalisar cewa suke yi bi ta da kulli ce kawai ta siyasa ake yi ma shugaban nasu.