Obama zai bar sojoji dubu goma a Afghanistan

Shugaba Obama na Amurka Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Obama na Amurka

Shugaba Obama ya bada sanarwar wani shiri na barin sojojin Amurka kimanin dubu goma a Afghanistan, koda bayan an janye galibin sojojin nan gaba a bana, lokacin da za a kawo karshen kai farmaki.

A wani jawabi a fadar White House, ya ce za bar sojojin Amurka dubu tara da dari takwas , kimanin kashi daya cikin uku na sojojin da yanzu haka ke kasar, su ci gaba da zama domin horas da dakarun Afghanistan, kuma idan ta kama su taimaka wajen yaki da ta'addanci game da kungiyar al-Qa'ida.

Ya ce daga nan ne za a rage yawan sojojin Amurka da kamar rabi a 2015, kafin a janye kusan daukacin sojojin shekara guda bayan nan. Wakilin BBC ya ce, bisa dukkan alamu an tsara jawabin ne , domin rufe wani babi ga Amurka, domin kawo karshen yakin, ta wata hanya da ya kira ta tsira da mutunci.