Saudi ta wargaza gungun 'yan ta'adda

Sarki Abdallah na Saudiyya
Image caption Saudi Arabia ta bayyana fushinta ga Amurka kan rashin taimakawa 'yan tawayen Syria

Gidan talabijin na Saudiyya ya ce hukumomin kasar sun wargaza wani gungun masu tayar da kayar baya, da ke shirya kai hari kan gine-ginen gwamnati.

An kuma kama mutane 60, mafi yawansu 'yan kasar ta Saudiyya, akwai kuma 'yan Yemen da Pakistan da kuma Plasdinawa.

Gidan talabijin din ya ambato ma'aikatar cikin gida ta kasar na cewa, gungun na da alaka da masu tsattsauran ra'ayi a Syria da kuma Yemen.

Saudiyyar na nuna damuwa game da karuwar 'yan kasarta da ke shiga yakin Syria, lamarin da ya sa ta ce tana daukar kungiyoyin da ke da alaka da AlQaeda, a matsayin kungiyoyin 'yan ta'adda.

Karin bayani