'Mata na haihuwa a yanayi mara kyau'

wasu 'yan gudun hijira suna barin gidajensu
Image caption Rikici da annoba iri daban-daban na sanya Mata da yara tserewa daga muhallansu

Rahoton kungiyar agaji ta Save the Children ya ce matsalar tashe-tashen hankula da annoba na tilasta wa mata zuwa gudun hijira ko kuma su haihu cikin yanayi mara kyau.

Rahoton da kungiyar ta fitar a ranar ya maida hankali a kan matsalar mace-macen mata masu juna biyu da kananan yara.

Rahoton ya kuma yi nazari kan batutuwan kula da lafiya da tattalin arziki gami da ilmi.

Kungiyar ta ce ko da yake wasu kasashen duniya sun samu nasarar rage mace-macen mata da kananan yara, amma wasu musammam kasashen da ke Kudu da hamadar sahara irinsu Najeriya ba su taka rawar a-zo-a-gani ba.