Shinawatra ta bayyana a gaban Kotu

Prime ministar Thailand Yingluck Shinawatra Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mis Shinawatra dai ta dade ta na fuskantar baraza daga al'umar kasar da suke bukatar da ta yi murabus daga mukaminta.

Prime Ministar Thaniland Yingluck Shinawatra ta bayyana a gaban kotun tsarin mulkin kasar, domin ta kare kanta kan zargin da ake mata na amfani da karfin ikon ta ba bisa ka'ida ba.

Wasu sanatoci ne suka shigar da koke kan cewa jam'iyyar Mis Yingluck ta amfana da maye gurbin shugaban rundunar tsaron kasar Thawil Plensri da ta yi , bayan ta ta dare mukamin Prime Ministar kasar a shekarar 2011.

Idan har aka same ta dumu-dumu da yin amfani da karfin ikonta ba bisa ka'ida ba, za a iya tsige ta daga mukaminta a kuma haramta mata shiga harkokin siyasa.