Mun sa hannu a Sudan ta kudu don kare gwamnati - Inji Museveni

Yoweri Museveni, Shugaban Uganda
Image caption Yoweri Museveni, Shugaban Uganda

Shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni, ya kare tsoma bakin da kasarsa ta yi a rikicin Sudan ta Kudu.

Dakarun Uganda na taimaka wa sojojin Sudan ta Kudu a fadan da suke yi da magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar.

A wata hira da BBC ,Mr Museveni yace, daya daga cikin hanyoyin hana juyin mulki shi ne gwamnatin da ta ga karfinta na neman karewa, ta bukaci taimakon wata gwamnatin da suke dasawa domin ta taimaka mata.