Ban Ki-Moon ya isa Sudan ta Kudu

Wasu 'yan gudun hijran Sudan ta Kudu Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rikicin Sudan ta Kudu ya raba mutane fiye da miliyan daya da muhallansu

Babban Sakataren Majlisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, ya isa Sudan ta kudu, domin tattaunawa da nufin kawo karshen yakin basasa a kasar.

Ana sa ran Mr Ban zai gana da shugaba Salva Kiir, wanda ya amince ya shiga tattaunawar kai tsaye da jagoran 'yan tawaye, Riek Machar.

Duk da cewa dakarunsa na kaddamar da hare-hare a garuruwan da ke hannun 'yan tawayen.

Yunkurin dakarun gwamnati na sake karbe iko da Bentiu, babban birnin jihar Unity mai arzikin man fetur ya ci tura, bayan gwabza fada da mayaka masu biyayya ga Mr. Machar.