Chibok: Dalibai sun kauracewa ajujuwa a Borno

Wasu 'yan matan Chibok
Image caption Kimanin 'yan mata sama da hamsin ne suka tsere daga hannun Boko Haram

Dalibai a jihar Borno, tungar kungiyar Boko Haram a Nigeria, sun ayyana ranar Laraba a matsayin ranar da za su kauracewa darussa, saboda sace 'yan matan Chibok.

Daliban da matasa za su yi amfani da ranar ce wajen yin addu'oi, domin gano inda 'yan mata sama da 200 suke da Boko Haram ta sace.

Sun kuma yi kira ga dalibai a fadin duniya su bi sahunsu wajen kauracewa ajujuwa a ranar Alhamis, domin sanya shugabannin duniya su matsa lamba ga Nigeria ta dauki matakan da suka dace na ceto 'yan matan.

Sama da makonni uku kenan da sace 'yan matan dalibai a makarantar sakandare da ke Chibok, kuma kawo yanzu babu wacce aka ceto.