Taron bunkasa tattalin arzikin Afrika

Taron bunkasa tattalin arzikin Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Taron bunkasa tattalin arzikin Najeriya

A ranar Laraba ne za a bude babban taron tattalin arzikin kasa na duniya akan Afrika, a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

Taron dai zai samu halartar shugabanni da 'yan kasuwa da wasu masu fada a ji akan manufofin tattalin arziki, domin tattauna yadda za a bunkasa tattalin arzikin nahiyar da duniya baki daya.

Za'a kwashe tsawon kwanaki uku ana gudanar da taron, wanda ake sa ran shugannin kasashe 13 za su halarta.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta rufe makarantu da kasuwanni har na tsawon kwanakin da za a yi taron, saboda dalilai na tsaro.

Wannan shi ne karon farko da wata kasa daga yammacin Afrika zata dauki bakuncin taron.