Chibok: Faransa, China, Birtaniya za su taimaka

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kimanin daraun Faransa 4000 ke aiki a kasashen Mali da jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Faransa ta bayyana aniyar taimakawa Najeriya da dakaru da kuma kwararru, domin nemo 'yan matan Chibok.

Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius ya ce shugaba Francois Hollande ya umarce shi ya shaida wa shugaban Najeriya cewa, kasar za ta iya amfani da dakaru da kayan yakin Faransan dake yankin, domin ceto 'yan matan.

Fabius ya shaida wa majalisar dokokin kasar a ranar Laraba cewa, ganin girma yanayin da ake ciki dole Faransa ta dauki mataki.

Ita ma Birtaniya za ta tura da karamar tawagar kwararru kan sha'anin tsaro Najeriya, domin nemo 'yan matan fiye da 200.

Sai dai Birtaniyar ta ce kwararrun ba za su shiga cikn daji da kansu, domin gano ida aka boye dalibai matan ba.

Kasar China ma ta mika nata tayin taimakon ga Najeriya, ta hanyar horar da dakarunta a fagen yaki da ta'addanci.

Wata sanarwa daga fadar shugaba Goodluck Jonathan ta ce kasar ta amince da tayin taimakon Birtaniyar da China.