'Yan matan Chibok ba sa kasashenmu'

Jagoran kungiyar Boko Hram Abubakar Shekau. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Baya ga 'yan mata 200 da aka sace a Chibok,an sace wasu karin matan 8 a kauyen Warabe da ke jihar ta Borno.

Gwamnatocin Chadi da Kamaru sun ce ba a tsallaka da wata daga cikin dalibai mata 200 da kungiyar Boko Haram ta sace zuwa cikin kasarsu ba.

Ministan Chadi yace hasashen da Amurka ta yi, na cewa ta yiwu masu tayar da kayar bayan sun tsallaka da wasu daga cikin 'yan matan daga arewa-maso-gabashin Najeriya zuwa Chadi domin sayar da su, zance ne mara tushe balle makama.

Ministan yada labaran Kamaru, Issa Tchiroma Bakari ya nanata kalamai irin wannan, ya kuma kara da cewa akwai cikakken tsaro a iyakar kasar da Najeriya.

Bayan sace dalibai matan a watan Afrilun da ya gabata, ana kyautata zaton kungiyar Boko Haram na boye ne da su a kungurmin dajin Sambisa.