Talauci a kasashen Afrika

Hakkin mallakar hoto PA

Wani sabon rahoto ya yi gargadin cewa yayinda tattalin arzikin kasashen duniya ke bunkasa, arzikin ba ya isa ga talakawansu.

A cikin rahotonta ta kowace shekara kungiyar African Progress Panel ta jadada cewa aikin noma muhimin abu ne wajen rage rashin dai daito tsakanin masu hanu da shuni da kuma talakawa.

Rahoton ya kuma ce nahiyar Afrika na asarar biliyoyin daloli sakamakon haramtattun ayyuka da wasu ke aikatawa a fanin su da kuma gandun daji .

Rahoton ya ce hakan kan taimakawa wasu tsiraru da suka rika aikata almundahana na amfana da su.