Amurka ta rufe ofishin jakadancinta a Yemen

Yemen Hakkin mallakar hoto Reuters

Amurka ta ce za ta rufe ofishin jakadancinta na takaitaccen lokaci a Yemen sakamakon yawan hare haren da ake kaiwa ma'aikatan diplomasiya.

Ma'aikatar cikin gida a Washington ta kira lamarin a matsayin matakin daukar rigakafi.

Yunkurin ya biyo bayan wani bafaranshe da aka kashe ranar litini dake aikin a wani kamfani dake samar da kariya ga tawagar kasashen Turai dake Yemen.

A cikin makwani biyu da suka gabata ne aka harbe tare da raunata wani jami'in diplomasiya na kasar Jamus a Sanaa babban birnin kasar yayinda aka yi kokarin sace shi.