Sambo Dasuki ya ziyarci Chibok

Sambo Dasuki Hakkin mallakar hoto The Will
Image caption Sambo Dasuki

Wata sanarwa da rundinar tsaron Najeriya ta fitar a yau ta ce mai baiwa shugaban kasa shawara ta fuskar tsaro, Kanar Sambo Dasuki Mairitaya, ya kai ziyara zuwa makarantar da aka sace 'yan matan nan sama da dari biyu a garin Chibok.

Tare da Sambo Dasukin akwai shugabannin rundinonin tsaron Najeriya da kuma Sufeto Janar na 'yan sandan kasar.

Sanarawr ta ce ziyarar wani bangare ne na yunkurin da hukumomin Najeriya ke ci gaba da yi na ceto 'yan matan da aka sace.

Jagoran sojan Najeriya ya yi kira ga mutanen yankin da su sanar da su duk wani bayani da suke da shi ko suka samu, wanda zai taimaka wajen ceto ‘yan matan da aka sace.