Dangote zai kashe dala biliyan biyu a arewa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Alhaji Aliko Dangote

Hamshakin dan kasuwa a Nigeria, Alhaji Aliko Dangote ya ce zai kashe dala biliyan biyu da miliyan dari uku wajen gina masana'antu a arewacin kasar.

Dangote wanda ya bayyana hakan a taron koli na tattalin arziki da ke gudana a Abuja, ya ce masana'antun za su dunga sarrafa shinkafa da kuma sikari.

Aliko Dangote na da masana'antar siminti mafi girma a nahiyar Afrika.

Dangote shi ne wanda ya fi kowa arziki a nahiyar Afrika, ya bayyana cewar kamfaninsa zai zuba jarin dala biliyan 12 a Nigeria da kuma karin dala biliyan hudu a wajen kasar, a cikin shekaru hudu masu zuwa.

Kasar China ta yi alkawarin kara zuba jari a Afrika.

A jawabinsa, Firayiministan China, Li Keqiang ya ce sun ware dala biliyan biyu don bunkasa ci gaban Afrika.

Karin bayani