'Batun Chibok zai kawo karshen ta'addanci'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya ce batun sace 'yan Matan chibok, ka iya kawo wani gagarumin sauyi a yaki da kungiyar Boko Haram.

A jawabin da ya gabatar a taron tattalin arzikin duniya kan Afrika a Abuja, Jonathan ya ce "Na yi imani cewa sace wadannan 'yan mata ka iya zama wani mafari na kawo karshen ta'addanci a Najeriya."

Ya kuma yaba wa Birtaniya da Amurka da China da Faransa a kan tayin taimakawa wajen kubutar da 'yan mata.

Sace 'yan mata fiye da 200 a Chibok makonni uku da suka gabata, ya harzuka jama'a a fadin duniya.

Kungiyar Boko Haram ta ce ita ce ta sace 'yan matan a ranar 14 ga watan Afrilu.

Abubakar Shekau, shugaban kungiyar ya yi barzanar sayar da 'yan matan a kasuwa.

Karin bayani