An samu karin hare-hare a Borno

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hare-hare na baya-bayan nan da aka kai a wasu yankunan jihar Borno ya yi sanadin mutuwar mutane da dama, bayan kara sace wasu 'yan mata 12 aka yi a ranar lahadin da ta wuce.

Ana kara samun bayanan akan hare-haren da ake zargin 'yan Kungiyar Boko Haram ne ke kaiwa a arewa maso yammacin Nageriya.

Mazauna yankin da 'yan Siyasa sun shaidawa BBC cewa an kai hare-hare a wurare daban-daban a jihar Borno a cikin 'yan kwanakin nan da ya yi sanadiyyar rasa rayukan daruruwan mutane.

Hari na baya-bayan nan da aka kai shi ne na garin Gamboru Nagla a ranar litinin da ta wuce, inda 'yan bindigar suka cinnawa kasuwar garin wuta.

Tuni dai mazauna yankin suka fara binne 'yan uwansu da suka rasu tun a ranar talata.

Garin Gamboru Ngala na na kusa da tsakiyar garin Maiduguri, inda dakarun Soji suke gudanar da ayyukansu na kokarin gano inda 'yan matan nan 200 da Kungiyar Boko Haram ta yi awon gaba da su a watan da ya gabata.

A bangare daya kuma an sake sace wasu karin matan goma sha daya a ranar lahadin da ta wuce, a lokacin da 'yan bindiga suka kai hari kauyen Waarabe da ke bakin iyakar Najeriya da Kamaru.