Kofi Annan ya soki Nigeria kan Chibok

Kofi Annan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar Boko Haram ta yi ikirarin sace 'yan matan kuma shugabanta Abubakar Shekau ya ce zai sayar da su

Tsohon sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, kofi Annan ya bayyana sace 'yan mata dalibai fiye da 200 a Chibok da cewa abin bakin ciki ne.

Haka kuma Mr. Annan ya soki gwamnatin Nigeria da sauran gwamnatocin nahiyar Afrika, kan rashin daukar matakai cikin gaggawa lokacin da lamarin ya faru.

Kana ya yi kira a gare su da su yi amfani da duk wata dama da suke da ita, na tabbatar da an kubutar da 'yan matan.

Kasashen Amurka da Birtaniya da Faransa da China, na daga cikin kasashen duniya da suka yi wa Najeriya tayin taimaka mata, a gano 'yan matan.