Jiragen saman soji na shawagi a Sambisa

Sojojin Najeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojojin Najeriya

Gwamnatin Nigeria ta ce jiragen sama na shawagi a yayinda sojojin kasa ke sa ido a dajin Sambisa da kuma iyakar kasar da Kamaru .

Rundunar 'yan sandan kasar ta ce za ta bada ladan naira miliyan 50 ga duk wani da ya taimaka wajen ceto 'yan matan Chibok.

Kasashen Amurka da Birtaniya da China da kuma Faransa za su tura da sojoji da kuma wata tawaga ta kwararu zuwa yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Kasashen za su samarwa kasar da tauraron dan adam da kuma naurar tattara bayanan siri da za su taimaka wajen ceto 'yan matan.

Kungiyar Boko Haram ta ce ita ce ta sace 'yan matan a makarantarsu da ke Chibok a jihar Borno.