Berlusconi ya fara aikin gwale-gwale

Hakkin mallakar hoto n
Image caption Mr Berlusconi zai rika shafe sa'oi hudu a kowana mako a gidan wanda ke kusa da Milan

Tsohon Firaministan Italiya Silvio Berlusconi, ya fara aikin yi wa al'umma hidima na shekara daya a wani gidan kula da tsofaffi.

A shekarar da ta gabata aka samu tsohon Firaministan da laifin kin biyan haraji, amma aka dauke masa hukuncin zaman gidan yari saboda tsarin shari'ar kasar ya yi sauki ga mutanen da suka haura shekaru saba'in.

Mr Berlusconi mai shekaru 77 zai ci gaba da jagorantar jam'iyyarsa a zaben Turai na wannan watan, amma kuma an takaita tafiye-tafiyensa cikin kasar ta Italiya sosai.