Kwararru daga Birtaniya sun isa Nigeria

Hakkin mallakar hoto GETTY IMAGES
Image caption Dakarun Birtaniya na aiken wanzar da zaman lafiya a Afganistan

Kwararru daga Birtaniya sun shiga sahun wata tawagar kwararru daga Amurka a Nigeria, domin taimakawa wajen ganowa da kuma ceto 'yan mata fiye da 200 da 'yan Boko Haram suka sace watan da ya wuce.

Tawagogin sun hada da hafsoshin soji da kwararru a sasanta wa da masu garkuwa da mutane.

Itama Amurka ta sanarda cewar tawagarta ta isa Nigeria.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Ms Marie Harf ta ce "Mun fara tura jami'ai don kara karfin tawagar mutanen da tuni suke a can. Ma'aikatar harkokin wajen za ta tura karin mutane 15 zuwa 20 da za su kara karfafa wa 50 zuwa 60 din da tuni suke da su a kasa a can".

Haka kuma Faransa da China suma za su aike da kwararrunsu zuwa Nigeria.

Tasirin boren 'yan Boko Haram a Nigeria ya kankane taron kwanaki biyu kan tattalin arzikin duniya da ake kamallawa a Abuja.

Taron dai ya hada shugabannin harkokin kasuwanci da manyan 'yan siyasa daga Afrika da sauran duniya wuri guda.

Karin bayani