Chibok: An yi zanga-zanga a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto Pajhwok
Image caption Ayyukan Boko Haram sun saba da na Islama

Ana ci gaba da zanga-zangar lumana a fadin duniya game da 'yan mata Chibok da aka sace fiye da makonni uku da suka wuce.

A birnin Bamyan na Afganistan, wasu 'yan mata da kungiyoyin kare hakkin bil adama sun bi sawun takwarorinsu a duniya wajen korafin cewar ya kamata 'yan Boko Haram su saki wadannan 'yan matan.

Kusan 'yan mata 80 ne a lardin Bamyan suka fito don yin Allahwadai da matakin 'yan Boko Haram na sace daliban a makarantar sakandare ta Chibok.

Daya daga cikin masu zanga-zangar Tayyeba Khawari, ta yi tur da wannan abu inda ta bukaci 'yan Boko Haram su kare hakkin bil adama.

Ismail Zaki, dan rajin kare hakkin bil adama ya ce Boko Haram na bayyana kanta a matsayin kungiya ta musulunci amma kuma ayyukanta sun saba da koyarwar addinnin Islama.

A karshen zanga-zangar, mutanen ciki hadda mataimakin gwamnan lardin sun yi kira a gaggauta sakin 'yan matan.

Karin bayani