Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 10/05/14

A Nigeria, Iyayen 'yan matan nan da aka sace a makarantar Chibok da ke Jihar Borno a arewa maso gabashin kasar suna cikin wani mayuwacin hali inda galibin su ba sa iya barci.

Har yanzu dai ba aga 'yan matan sama da dari biyu ba abinda ya jawo hankulan kasashen Duniya.

Amurka ma dai ta ce zata bada taimako ga Najeriya yadda za a ceto 'yan matan.

Haka ma Birtaniya da Faransa da China duka sun yunkurin bada tallafi.

Makwonni sama da uku ke nan da aka sace 'yan matan amma har yanzu kamar an aiki bawa garinsu.

Ko da yake dai Gwamnatin Najeriya na cewa tana yunkurin ceto 'yan matan.

Tuni dai Kungiyar Boko Haram ta dauki alhakkin sace 'yan matan.

A filinmu na Gane mani Hanya na wannan mako, wakilinmu Mustapha Muhammad ya yi tattaunawa ta musamman da wasu iyayen 'yan matan da aka sace; wadanda suka nemi ya sakaya sunayensu. Bari dai in hada ku da Mustapha da Bakin nasa.