Matar Obama za ta yi jawabi kan Najeriya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Michelle Obama na matukar sukan 'yan Boko Haram da suka sace 'yan matan garin Chibok, a Najeriya

A wani lamari na ba safai ba, mai dakin shugaba Obama, Michelle za ta gabatar da jawabin da shugaban yake yi mako-mako ranar Asabar a kan sace 'yan matan Chibok a Najeriya.

Galibi dai matayen shugabannin kasashe sukan kauce wa furta kalamai da suka shafi harkokin kasashen waje.

A farkon makon nan ne ma ta sanya wani hoton da ta dauka a fadar Amurkan ta White House, a shafin twitter, tana rike da wata alama da ke kiran a dawo da 'yan matan.

Karin bayani