Taron tattalin arziki ya zo karshe a Nigeria

Shugaban Nigeria na jawabi a wajen taron a Abuja Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Nigeria ya yi fatan ceton 'yan matan Chibok zai kai ga karshen Boko Haram

Taron tattalin arzikin duniya kan Afirka a Abuja, da ya hada hamshakan 'yan kasuwa da shugabannin kasashe daga Afrika da ma duniya ya kawo karshe.

An tsaurara matakan tsaro yayin taron na yini uku, wanda tarzomar 'yan tada-kayar-baya a yankin arewa maso gabashin kasar, gami da sace 'yan matan Chibok fiye da 200 da Boko Haram ta yi, suka dusashe tasirinsa.

Wani ayarin sojoji da kwararrun jami'an sirrin Amurka ya isa Najeriya, kuma yana shirin fara aiki domin gano inda ake tsare da 'yan matan.

Haka zalika, Burtaniya, Faransa da China su ma za su tura nasu kwararrun domin taimaka wa yunkurin ceto 'yan matan.

An yi ta sukar lamirin Hukumomin Nijeriya a kan tafiyar hawainiya wajen ganowa tare da kubutar da 'yan matan da aka sace

Karin bayani