Za a fara tattaunawa kan Sudan ta Kudu

Image caption A watan Janairu bangarorin biyu suka sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya, da ta kasa kawo karshen rikicin.

Za a fara tattaunawar zaman lafiya tsakanin shugaban Sudan ta Kudu da jagoran 'yan tawaye Riek Machar nan da 'yan sa'oi kadan.

Ganawar ta kwana daya, wadda za a yi a Ethiopia wato Habasha, ita ce karon farko da mutanen biyu za su gana gaba da gaba tun lokacin da fada ya barke a Sudan ta Kudu a watan Disamba.

Dubban mutane aka kashe, wasu kuma sama da miliyan daya suka rasa muhallansu.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya zargi bangarorin biyu da aikata laifin cin zarafin bil'adama.

Wanda ya hada da kisan kare dangi, da kama mata ana mayar da su kwarkwara da kuma fyade na gungu.

Jakadiyar musamman ta majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudun Hilde Johnson ta ce idan ba a samu cigaba a tattaunawar ba, rikicin zai kara baci.