An cimma yarjejeniya a Sudan ta Kudu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sun kuma bayar da dama a kai kayan agaji a wuraren da ake bukata da kuma kafa gwamnatin rikon kwarya.

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir, da jagoran 'yan tawaye, Riek Machar sun sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya ta dakatar da bude wuta cikin sa'oi 24.

Kungiyar kasashen Gabashin Afrika, IGAD da shugabanta, Frai ministan Ethiopia, Hailemariam Desalegan, su suka shiga tsakani a zaman yarjejeniyar.

Sai dai kuma wakilin BBC a wurin tattaunawar ya ce abin jira a gani yanzu shi ne, yadda yarjejeniyar za ta dore.

Iidan aka yi la'akari da mummunar gabar kabilancin da ke Sudan ta Kudun, inda aka kashe dubban jama'a, wasu sama da miliyan daya suka rasa muhallinsu tun lokacin da rikicin kasar na yanzu ya barke a watan Disamba.