Majalisar Dinkin Duniya ta damu kan matan Chibok

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kwamitin tsaron ya yi kira da a dauki matakan hukunta masu kai harin tare da neman sanya musu takunkumi.

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi matukar nuna damuwa tare da kakkausar suka kan kame 'yan matan Chibok da ke Maiduguri a Njeriya, da 'yan Boko Haram suka yi.

Kwamitin ya kuma yi irin wannnan suka kan sauran munanan hare-haren da 'yan kungiyar ta Boko Haram ke kaiwa.

Dama dai tuni kwararru kan harkokin tsaro daga kasashen Amurka da Birtaniya da kuma Faransa suka hallara a Najeriyar domin taimakawa a gano 'yan matan.

Amurka da Birtaniyan sun kuma ce suna duba bukatar da Najeriyar ta gabatar musu ta neman agajinsu da jirgin sama na gudanar da bincike.