An gano karin gawarwaki 24 a jirgin Libya

Hakkin mallakar hoto AP

Jami'an Libya sun ce sun gano wasu karin gawarwaki 24 daga cikin wani jirgin ruwan da ya kife a tekun kasar a makon jiya.

Yanzu dai an tabbatadda cewa akalla mutane 36 ne daga cikin wadan da ke jirgin, ruwa ya ci, yayinda kuma ake neman 40.

Masana sun ce yawan 'yan Syria da 'yan Afrika da suka yi kokarin tsallaka tekun Mediterranean don su shiga Turai a bana, abune da ba a taba ganin irin sa ba.

Tun farko, ministan harkokin cikin gidan Libyar ya yi barazanar taimakawa mutanen da ke bi ta kasar su shiga Turai, idan Tarayyar Turai bata taimakwa kasar shawo kan matsalar ba.

Shugaban rundunar sojin ruwan Italiya yace gungun masu safarar mutane ne ke cutar mutane inda suke sasu a jiragen ruwan da basu da kyau