Jirgin Najeriya ya yi saukar gaggawa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane biyun da ke cikin jirgin sun tsallake rijiya da baya

Wani karamin jirgin sama na Najeriya yayi saukar gaggawa a wani kauye a jihar Dosso ta Jamhuriyar Nijar.

Bayanai sun tabbatar da cewa ba abin da ya samu mutane biyun da ke cikin jirgin.

Amma kuma jirgin ya baci sosai kasancewar a wani daji da ke dab da kogin Kwara na kasar ya sauka.

Lamarin ya faru ne da daren Asabar dinnan a kauyen da ke da nisan kusan kilomita 100 daga birnin Dosso.

Karin bayani