Sudan ta Kudu: an karya yarjejeniya

Hakkin mallakar hoto Getty AFP
Image caption Riek Machar ya zargi Shugaba Salva Kiir da haddasa gabar kabilanci.

Jagoran 'yan tawayen Sudan ta Kudu Riek Machar, ya ce har yanzu yana mutunta yarjejeniyar zaman lafiyar da suka kulla da Shugaba Salva Kiir na kasar duk da gwamnati ta saba sulhun in ji shi.

Ya ce, ''gwamnati ce take kai mana hare-hare duk tsawon wadannan watanni, tun ranar 23 ga watan Janairu

Da yake magana da BBC, Mr Machar , ya ce yana son su kara yin wasu sharuddan da gwamnatin bayan yarjejeniyar da suka yi ranar Juma'a.

Amma kuma ya ce, shugaban kasar ba shi da iko da wasu dakarun da ke mara wa gwamnatinsa baya, kamar sojojin Uganda da mayakan Darfur.