Za a yi zaben raba gardama a gabashin Ukraine

Zaben raba gardama a gabashin Ukraine
Image caption Zaben raba gardama a gabashin Ukraine

Nan gaba a yau ne masu fafitikar goyon bayan Rasha dake dukkan fadin gabashin Ukraine suka shirya yin zaben raba gardama kan mulkin kai.

Za su gudanar da kuri'ar ne sakamakon tayar da kayar bayan da 'yan bindiga masu goyon bayan Rasha suka yi, da kuma bata kashi tsakanin 'yan bindigar da dakarun gwamnatin Ukraine.

Gwamnatin Ukraine da Shugabannin kasashen yammacin duniya sun yi Allah Wadai da zaben raba gardama jama'a da cewa haramtacce ne.

Shugaban hukumar zaben a Donetsk, Roman Lygan ya ce babu karancin masu aikin sa kai da za su taimaka wajen kasa kuri'ar samun 'yancin cin gashin kai daga Kiev.

Shugaban wucin gadi na kasar Ukraine Oleksandr Turchynov ya gargadi mutanen gabashin kasar game fitowa kada kuri'un.

Mr Turchynov ya kara da cewa zaben raba gardamar da masu tada kayar bayan suka shirya a biranen Donetsk da Luhansk da cewa tamkar yiwa kai karan tsaye ne.