Nyanya: Gwamnonin APC sun bada tallafi

  • 12 Mayu 2014
Image copyright AFP
Image caption Mutane kusan 88 ne suka mutu a hare-haren Nyanya

Gwamnonin jam'iyyar APC mai hamayya a Nigeria sun ce sun bada gadunmuwar naira miliyan 100 ga mutanen da hare- haren Nyanya ya shafa da kuma iyalan wadanda suka rasa rayukan su.

Shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar kuma gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ne ya bayyana haka a wajen taron da gwamnonin suke gudanarwa a Kano.

Gwamnonin sun kuma nuna damuwa kan yadda har yanzu aka gaza kubutar da 'yan matan da aka sace a garin Chibok na jihar Borno.

A cewarsu wajibi ne hukumomi su hada kai dan ceto 'yan matan, ba tare da la'akari da bambamcin siyasa ba.

Taron wanda ake gudanar da shi a fadar gwamnatin Kano ya samu halartar kusan duka gwamnonin jam'iyyar da kuma jiga jigan jam'iyyar na kasa.

Karin bayani