Chadi ta rufe kan iyakar ta da CAR

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shuugaban Chadi, Idriss Deby

Kasar Chadi ta sanar da cewa za ta rufe kan iyakar ta da Jamhuriyar tsakiyar Afirka har illa ma sha Allahu.

Matakin ya zo ne yayin da shugaban Chadi, Idriss Deby yake ziyarar kudancin kasar sa da ke iyaka da Jamhuriyar tsakiyar Afirka.

A watan da ya gabata kasar Chadi ta janye dakarunta na kiyaye zaman lafiya daga Jamhuriyar tsakiyar Afirka wadda ta sha fama da rikicin kabilanci dana addini a bara.

Janyewar a wancan lokaci ta biyo bayan zargin cewa sojojin Chadi suna taimakawa mayaka musulmi zargin da gwamnatin Chadin ta musanta.

Karin bayani