'Jamhuriyar Donetsk' na son hadewa da Rasha

Mayakan sa kai a gabashin Ukraine Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan sa kai a gabashin Ukraine

'Yan bindiga masu goyon bayan Rasha a gabashin Ukraine sun ce suna son hadewa da Rasha bayan zaben raba gardamar 'yancin cin gashin kai da suka gudanar a ranar Lahadi.

Shugaban da ya ayyana kansa a matsayin jagoran yankin da suka kira Jamhuriyar al'ummar Donetsk Dennis Pushilin shine ya sanar da hakan ga manema labarai.

Ya ce suna kira ga Tarayyar Rasha ta duba batun jama'ar Jamhuriyar Donetsk na zama cikin yankin kasar Rasha.

Gwamnatin Ukraine a birnin Kiev ta yi watsi da zaben wanda ta baiyana da cewa haramtacce ne.

Amurka da kungiyar tarayyar Turai ma sun yi fatali da zaben raba gardamar a gabashin Ukraine da cewa ba shi da wani halacci.