Boko Haram: An gane mata uku a bidiyo

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kimanin 'yan mata 130 ne aka nuna a bidiyon na Boko Haram sanye da hijabai

Wasu 'yan makarantar Chibok da suka tsere tun da fari, sun shaida abokan karatunsu uku a bidiyon da kungiyar Boko Haram ta fitar a ranar Litinin.

Wani daga cikin shugaban al'ummar garin Chibok ne ya shaida wa BBC hakan.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ma ya ce, wata shugabar kungiyar iyayen yara da dalibai ta makarantar ta gane 'yarta a bidiyon.

Yayin da wasu suka ce sun ji dadin ganin 'yan matan a raye, a bidiyon da Boko Haram din ta fitar, wasu iyaye da 'yan uwan 'yan matan sun nuna bacin ransu game da halin da 'yan matan ke ciki.