Jamus za ta sasanta rikicin Ukraine

Masu zanga-zanga a Kiev Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kasar ukraine dai ba ta samu daidaito ba tun bayan habarar da shugaban Viktor Yanukovych

A yau ne Ministan harkokin wajen Jamus zai isa Ukraine domin tattaunawa dan kawo karshen rikicin da ake yi a gabashin kasar.

Frank Walter Steinmeir zai ziyarci babban birnin kasar Kiev kuma watakil ma ya isa har yammacin birnin.

Duk dai a kokarin da yake na ganin ya shawo kan gwamantin kasar da kuma masu fafutuka a garuruwan Donestsk da kuma Lugansk su yadda su sasanta rikicin da ke tsakaninsu.

A jiya litinin ne masu fafutukar suka bayyana kansu da wadanda suke son hadewa da Rasha bayan an gama kada kuri'ar raba gardama.

A bangare daya kuma Amurka da tarayyar Turai da kuma gwamnatin Kiev sun yi watsi da kuri'ar su na mai cewa haramtacciya ce.