Jiragen Amurka na shawagi a Nigeria

Sojojin Amurka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ita ma Birtaniya an bukaci ta samar da jiragen leken asiri ta sama

Amurka ta sanar da cewa ta fara shawagi da jiragen sama na leken asiri a Najeriya, a yunkurin ceton 'yan matan nan na Chibok.

An sace 'yan matan fiye da 200 ne daga makarantar 'yan mata a garin Chibok da ke kudancin jihar Borno makwanni hudu da suka wuce.

Amurkar ta kara da cewa ta ba Najeriya bayanan hotuna na tauraron dan Adam.

Kakakin fadar White House Jay Carney ya shaidawa BBC cewa tawagarsu da ta hada da wakilai daga ma'aikatar harkokin wajen kasar da ma'aikatar tsaro da hukumar binciken manyan lefuka ta FBI da sauran hukumomi na ofishin jakadancin kasar da ke Abuja.