Jonathan na so a tsawaita dokar ta-baci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar Boko Haram ta ci gaba da kai hare-hare duk da dokar ta-baci a Borno da Yobe da Adamawa

Shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan, ya bukaci majalisar dattawan kasar ta tsawaita dokar ta-bacin da ya sanya a jihohin Borno da Adamawa da Yobe zuwa watanni shida.

A wata takarda da ya aikewa majalisar dattawan kasar wacce shugaban majalisar, Sanata David Mark, ya karanta a zauren majalisar, shugaba Jonathan ya ce ya bukaci a tsawaita dokar ta-bacin ne domin a tabbatar da tsaro a jihohin.

A ranar Laraba ne dai wa'adin dokar-tacin zai kare.

Da ma shugaban ya ce yana tataunawa domin yiwuwar tsawaita wa'adin dokar ta-bacin.

Jihohin na Borno da Yobe da Adamawa dai sun kasance a cikin dokar ta-baci shekara guda kenan, amma duk da haka hare-haren da 'yan Boko Haram ke kai wa sai karuwa suke yi.

Al'ummar yankin sun sha sukar gwamnati game da rashin daukar kwakkwaran mataki na magance matsalar tsaro da ta addabi yankin.

Karin bayani