Nigeria na yin nazari kan bidiyon Boko haram

Image caption Najriya na duba duk zabi na ceto 'yan mata

Gwamnatin Nigeria ta ce tana nazari kan gundarin bidiyon da Boko Haram ta fitar da kuma sakon da ya kunsa.

Wata sanarwar da shugaban hukumar wayar da kai ta kasa, Mike Omeri ya aikawa BBC ta ce, gwamnati za ta ci gaba da bin duk wasu zabi domin ceto 'yan matan nan da aka sace su dawo gidajensu cikin koshin lafiya.

Amurka dai ta ce akalla mutane 30 daga ma'aikatar tsaro da Hukumar FBI na Najeriya.

A ranar Litinin ne dai Kungiyar Boko Haram ta fitar da wani sabon bidiyo, inda ta ke neman a yi musayar da'yan matan da mayakanta.

Karin bayani