Nijar na maraba da taro kan Boko Haram

Bazoum Mohamed Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban 'yan gudun hijira da suka tsere wa rikicin Boko Haram na jamhuriyar Nijar

A jamhuriyar Nijar hukumomin kasar sun ce suna goyon bayan shugaban Faransa, Francois Hollande na shirya taron koli kan Boko Haram.

A ranar Asabar mai zuwa ne Faransar ta shirya daukar bakuncin taron, inda Najeriya da makwabtanta karkashin jagorancin kasar zasu tattauna kan matsalar Boko Haram.

Ministan harkokin wajen Nijar Bazoum Mohamed ya ce taron wata dama ce ga makwabtan Najeriya, su bayar da shawarwari game da matakan da suke ganin zai taimaka wajen shawo kan matsalar.

Kasar Faransa na daga cikin kasashen duniya da ke taimaka wa Najeriya wajen gano 'yan matan Chibok da Boko Haram ta sace.