Man U: Giggs da Van Gaal za su gana

Louis Van Gaal Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manchester Utd ta zamo ce ta zamo ta bakwai a gasar premier da aka kammala

A kokarin da kungiyar Manchester United ke yi na yanke shawara kan shugabancin kulob din, Ryan Giggs da Van Gaal za su gana a Netherlands a ranar laraba.

Van Gaal mai shekaru 62 kuma kocin kasar Polland, a yanzu haka ana shirin nada shi a matsayin kocin United, za kuma su tattauna da Giggs kan batun da ya shafi horarwa.

Amma kocin rikon kwaryar kulob din wato Giggs, ya ce ba shi da tabbacin ci gaba da buga wasa a kakar gasa ta badi.

Yanzu haka dai Van Gaal yana lura da 'yan wasan kasar Netherlands, a filin wasan na Hoenderloo inda suke horo, a shirye-shiryen tunkarar gasar cin kofin duniya.