An yi muhawara kan tsawaita dokar-ta-baci

Hakkin mallakar hoto aliyu
Image caption A bisa kundin tsarin mulkin kasar dai dokar ta bacin ba za ta iya zarce watanni 6 ba; har sai majalisar kasar ta amince da a tsawaita ta.

Majalisar wakillan Najeriya ta yi muhawara a yau Laraba kan bukatar da shugaba Goodluck Jonathan ya gabatar mata ta neman amincewa da tsawaita dokar-ta-baci a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.

Bayan kwashe sa'ao fiye da uku ana muhawarar daga karshe majalisar ta jinkirta jefa kuria kan batun zuwa ranar Alhamis bayan ta saurari bahasi daga manyan hafsoshin tsaron kasar.

''Shugabancin wannan majalisar ya amince cewa za mu kada kuria kan wannan bukatar a gobe, amma kafin wannan muna sa ran manyan hafsoshin hukumomin tsaro su bayyana gaban majalisar goben domin su sanar da ita inda aka kai a kokarin kubutar da 'yan matan Chibok da kuma irin ci gaban da dokar-ta-bacin ta kawo ya zuwa yanzu.'' inji Kakakin majalisar Aminu Waziri Tambuwal.

A yayin zaman muhawarar dai 'yan majalisar sun kasu zuwa gida uku - wato masu son a tsawaita dokar zuwa watanni shida kamar yadda shugaban kasar ya bukata, da masu son a tsawaita amma zuwa watanni uku kawai da kuma wadanda ke adawa da tsawaita dokar ga baki daya.

Karin bayani