Mutane 2 sun rasa rayukansu a Bankok

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mutane 2 sun mutu a zanga-zangar Bankok

A kalla mutane biyu sun rasa rayukansu a lokacin da aka harba gurneti a sansanin zanga-zangar kin jini gwamnati a babban birnin kasar Thailand wato Bangkok.

Mutane dari biyu kuma sun jikkata, masu zanga-zangar dai na bukatar majalisar dokokin kasar ta tsige shugabannin rikon na gwamnatin Thailand tare da nada sabon Firai Minista.

A makon da ya gabata ne kotun tsarin mulkin kasar ta bada odar Firai Minista Yingluck Shinawatra ta yi murabus daga mukaminta saboda samun ta da laifin yin amfani da karfin iko ba bisa ka'ida ba.

Daga watan Nuwanbar bara zuwa wannan watan na Mayu akalla mutane 77 ne suka rasa rayukansu a rigingimun da suke da nasaba da siyasa a kasar Thailand.

Karin bayani