Majalisar wakilai ta amince da dokar ta-baci

Gini majalisar dokokin Najeriya Hakkin mallakar hoto aliyu
Image caption 'Yan majalisar da suka fito daga yankin da aka sa dokar na adawa da karin wa'adin

Majalisar wakilai Nigeria ta amince a kara wa'adin dokar ta-baci da watanni shida, bayan wadanda ke goyon baya sun yi rinjaye.

Majalisar ta kada kuri'ar ne bayan ta yi wata ganawar sirri da manyan hafsoshin sojin kasar.

Hafoshin sojin da kuma manyan jam'an tsaron kasar sun yi wa 'yan majalisar bayani game da yanayin tsaro a kasar.

A ranar Talata da ta gabata ne Shugaba Goodluck ya tura bukatar karin wa'adin dokar ta-bacin, a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa a karo na uku.