An tuhumi matukan jirgin Korea da sakaci

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jirgin Korea ta kudu ya bar mutane da alhinin mutuwa

Masu shigar da kara a Korea ta Kudu sun tuhumi hudu daga cikin ma'aikatan jirgin ruwan nan da ya nutse da laifin sakaci wajen mutuwar mutanen jirgin.

Ana zarginsu da barin aikinsu tare da fadawa Fasinjojin jirgin su zazzauna.

Fiye da mutane 300 ne suka rasa rayukansu a lokacin da jirgin ya nutse, yawancinsu kananan yara 'yan makarantar sakandare da ke kusa da Seol babban birnin kasar.

Jirgin ruwan ya taso ne daga Incheon zuwa tsuburin Jeju, dauke da fasinjoji fiye da 470.

Karin bayani