Za a yi yajin aiki a Turkiyya

Wadanda suka tsira da ransu a mahakar ma'adinai ta Soma. Hakkin mallakar hoto
Image caption Kimanin sama da mutane dari ne ke makale a kasa, rashin iska da wutar da ke tashi ta hana ma'aikatab ceto isa gare su.

Kungiyar kwadago a kasar Turkiyya ta yi kira da a tafi yajin aiki na kwana daya don nuna rashin jin dadi kan bala'i mafi muni da mahakar ma'adinan kasar ta fuskanta.

Shugabannin kungiyoyin sun yi korafin cewa sayar da hannayen jari a fannin ma'adinai a 'yan shekarun nan ya janyo tabarbarewar kariyar lafiyar ma'aikatan wajen.

Shugabannin sun kuma yi kira ga mambobin su da su sanya bakaken kaya tare da yin machi zuwa ma'aikatar kwadagon kasar.

Wani mai aikin ceto ya shaidawa BBC cewa isa wurin wadanda suke raye ya na neman gagararsu.

Ya ce akwai wuraren da ba za su iya isa ba a cin mahakar ma'adinan, wuta na ci gaba da tashi a karkashin kasa, sannan sinadrin Carbon Monoxide na karuwa.

Wasu lokutan dole suke dawo da ma'aikatansu, ana iya ganin gungun mutanen a kasa amma ba damar isa wurinsu.

Ya zuwa yanzu dai Mutane 274 aka tabbatar da sun rasa rayukansu a mahakar ma'adinan Coal da ke garin Soma.