Modi zai zama sabon Firaministan India

Image caption Nerandra Modi

Jam'iyyar BJP ta masu kishin addinin Hindu ta lashe babban zaben da aka gudanar a India.

Kuri'un da aka kidaya ya zuwa yanzu, sun nuna cewa jam'iyyar ta BJP wadda Narendra Modi ke jagoranta, tana kan hanyar samun gagarumar nasarar da wata jam'iyya ba ta samu a kasar ba a cikin shekaru 30 da suka wuce.

Tuni dai magoya bayan jam'iyyar ta BJP suka fara shagulgular murnar nasarar da suka samu.

Shugaban jam'iyyar ta BJP, Rajnath Singh, ya bayyana cewa India ta shiga wani sabon babi, kuma ya yi alkawarin taimakawa dukan bangarorin al'ummar kasar.

Sai dai wani wakilin BBC a India, ya ce yanzu kabilu 'yan tsiraru a kasar, za su shiga damuwa, saboda suna ganin cewa akidar jam'iyyar ta BJP tana yin barazana ga tsaron lafiyarsu.

Karin bayani